in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a samar da kyakkyawan muhallin kasuwanci don sabbin kamfanoni su samu ci gaba cikin adalci
2014-07-28 10:48:32 cri

Firaministan kasar Sin Mista Li Keqiang ya yi nuni da cewa, za a samar da kyakkyawan muhallin kasuwanci, wanda zai baiwa sabbin kamfanoni damar samun bunkasuwa cikin adalci.

Mr. Li ya ce za a cimma wannan buri ne ta hanyar rarraba ikon gudanarwa da mulki zuwa matakai na kasa, da kuma gudanar da kwaskwarima ga tsarin rajistar harkokin kasuwanci a kasar.

Firaminista Li ya bayyana hakan ne a wani taron shugabannin sabbin kamfanoni, wadanda yawansu ya kai miliyan 1.68 a farkon watanni 6 na shekarar bana, adadin da ya karu da kaso 57 bisa dari idan an kwatanta da na shekarar bara. Kaza lika Mr. Li ya bayyana cewa, dalilin cimma nasarar raya tattalin arziki yadda ya kamata a tsakanin watanni 6 na farkon shekarar bana, da kuma yadda yawan guraben ayyukan da aka samar ya zarce na makamancin lokaci a bara, duk da manyan matsaloli da aka fuskanta a wannan fanni, shi ne yadda gwamnatin kasar Sin ta rarraba ikon gudanarwa da mulki zuwa matakai na kasa, da kuma gudanar da aikin kwaskwarima da kasar ke yi a fannonin da hakan ya shafa.

A wajen taron, Mista Li ya ce, za a ci gaba da rarraba ikon gudanarwa da mulki zuwa matakai na kasa, a kokarin kago wani kyakkyawan muhallin kasuwanci. Kuma a magance ka'idoji marasa ma'ana dake kawo cikas ga bunkasuwar kamfanoni.

Bugu da kari, a cewarsa, za a kara nuna goyon baya ga sabbin kamfanoni a fannonin kudi da ayyukan ba da hidima, haka kuma za a yi nazari kan yadda za a mara wa kananan sabbin kamfanoni baya ta fuskar manufa. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China