Cikin wannan sharhi, Wang Yi ya bayyana cewa, ra'ayin kasar Japan kan tarihinta na yakin da bai cancanta ba ya sha bamban da ra'ayin kasashen Turai kan yakin Nazi, wanda kasar Germany ta dauki alhakin laifin yakin da ta aikata.
Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da neman bunkasuwarta ta hanyoyin zaman lafiya, hadin gwiwa da kuma cimma moriyar juna, kuma za ta ci gaba da ba da gudummawa cikin harkokin kasa da kasa yadda ya kamata a matsayin wata babbar kasa, a sa'i daya kuma za ta kiyaye dangantakar abokantaka dake tsakaninta da kasashe makwabtaka kamar yadda ta saba yi. Wannan shi ne alkawarin da kasar Sin ta yi wa kasa da kasa kuma ba zai canja ba. (Maryam)