in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya bayyana ra'ayinsa kan yanayin tekun Kuduncin kasa
2014-02-15 17:13:16 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana ra'ayi, da manufofin kasar Sin kan yanayin da ake ciki a yankin tekun Kuduncin kasar ta Sin.

Mr. Wang ya bayyana hakan ne a jiya Jumma'a, yayin da yake ganawa da takwaransa na Amurka John Kerry. Wang ya ce, yanzu haka akwai kyakkyawan yanayin zaman lafiya a wannan yanki. Kuma Sin tana da karfi da kwarin gwiwar ci gaba da tabbatar da zaman lafiyar da ake fatan gani, da hadin gwiwar sauran kasashen kungiyar kudu maso gabashin Asiya.

Baya ga wannan, game da batun zirga-zirga cikin 'yancin a wannan yanki na tekun Kuduncin kasar Sin, har kwanan gobe kowace kasa na da ikon yin hakan bisa dokoki tabbatattu. Ya ce Sin da kasashen kungiyar kudu maso gabashin Asiya, na kokarin fayyace ayyukan bangarorin masu ruwa da tsaki a wannan shiyya, da karfafa hakikanin hadin gwiwa a yankin teku, tare da sa kaimi ga gudanar da shawarwari don tabbatar da wata ka'idar da za a bi yayin da ake gudanar da ayyuka a yankin tekun Kudu .

Har wa yau Mr. Wang ya ce kasar sa na da ikon mallakar tsibiran tekun Kudu da na yankin tekun dake kewayensu bisa tarihi da kuma dokoki. Ya ce wasu kasashe sun mallaki wasu tsibiran dake yankin tekun Kudancin Sin ba bisa ka'ida ba, a shekaru 70 na karnin da ya shude, wanda hakan ne ya haifar da matsalar da ake fuskanta a yanzu. Sai dai duk da haka, Sin tana tsayawa tsayin daka wajen daidaita matsalar ta hanyar yin shawarwari, da kasashen da abin ya shafa kai tsaye, da zummar shawo kan matsalar cikin lumana.

Dadin dadawa, Wang ya bayyana cewa a kwanan baya wasu mutane sun rika yada jita-jita a kasashe daban daban, suna zuzuta matsalar tekun Kuduncin, sama da yanayin da ake ciki a yanzu.Ya ce game da hakan, Sin ko alama ba za ta amince da irin wannan shaci-fadi ba.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China