Qin Gang ya ce zabar kasashen Afirka da ministan ya yi don kai ziyararsa ta farko a sabuwar shekara, ya nuna yadda kasar Sin ke daukar Afirka da muhimmanci.
Ya ce, ya kasance al'ada ga ministocin harkokin wajen kasar Sin tun a shekara ta 1991, su fara ziyartar kasashen Afirka a kowace sabuwar shekara, kuma wannan ita ce ziyara ta farko da sabon ministan harkokin wajen kasar ta Sin ya kai kasashen Afirka da ke kudu da hamadar sahara, tun lokacin da sabbin shugabannin kasar suka kama aiki.
Mr Qin Gang, ya ce kasar Sin ta yi imanin cewa, ziyarar za ta kara zurfafa dangantakar abokanta, mutunta juna da hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim)