Wang Yi ya furta cewa, dukkan kasashen Afrika, mambobi kasashen duniya ne, kuma suna da hakkin raya kansu, kuma akwai makoma mai haske wajen raya su. Ya ce, idan babu ci gaban Afrika, ba za a samu wadata a kasashen duniya ba. Ya kamata kasashen duniya su taimakawa kasashen Afrika. Ya ci gaba da bayyana cewa, kasar Sin ta zama daya daga cikin kasashen da suke taimakawa kasashen Afrika a farko, kuma irin taimakon da Sin ta bayar, sun kasance masu amfani, kuma kasashen duniya sun amince da wannan. Dalilin da ya sa hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika zai iya haifar da babban tasiri shi ne, yayin da Sin take raya hakikanin hadin gwiwa da kasashen Afrika, kullum ta kan nace wajen bin hanyar cikin daidaito da rike amana, da bisa sahihiyar zuciya. (Bako)