Ministan ya ce, Sin na maraba da taron da za a kira karo na biyu kan batun syria a birnin Geneva, wanda ya kasance wata muhimmiyar dama ta daidaita batun. Don haka, ya kamata a tsaya kan wadannan manufofi biyar, na farko a daidaita batun Syria a siyasance, a bar jama'ar Syria su tabbatar da makomar kasarsu, a inganta wani cikakken shirin mika mulki da zai kunshi kowa da kowa, a tabbatar da sulhu da hadin kai tsakanin al'ummar Syria, kana na biyar a samar da agajin jin kai a Syria da kasashe makwabtanta.
Ministan ya jaddada cewa, taron Geneva matakin farko ne na shawarwarin, amma ya kamata a ci gaba da yin shawarwari bayan taron. Don haka, ya zama wajibi a tabbatar da wani tsari na bin diddigin taron. Har wa yau, ministan ya ce, Sin tana fatan sassa daban daban na Syria su yi la'akari da makomar kasar da moriyar al'ummar ta, su ba da hadin kai ga juna, su daidaita matsalar da ake fuskanta bisa la'akari da halin da kasar ke ciki da kuma moriyar sassan daban daban.(Lubabatu)