in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya kammala ziyararsa a kasashen Afirka guda hudu
2014-01-12 17:04:56 cri
A ran 11 ga wata da dare, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kammala ziyarar aikinsa a kasar Senegal, wanda ta kawo karshen rangadin aiki na kwanaki shida a kasashen Afirka hudu. Ziyarar dai ita ce karo ta farko da ministan harkokin wajen kasar Sin ya kai a kasashen ketare na shekarar bana.

Wang Yi ya fara ziyarar aikinsa a kasar Segenal a ran 10 ga watan Janairu, inda ya gana da shugaban kasar Macky Sall da kuma firaministar kasar Aminata Toure.

A yayin ganawarsu, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana son ci gaba da bunkasa dangantakar abokantaka dake tsakaninta da kasar Senegal bisa manyan tsare-tsare, karfafa hadin gwiwar kasashen biyu bisa fannoni daban daban, da kuma sa kaimi ga kamfanoni masu inganci na kasar Sin da su zuba jari a kasar Senegal, ta yadda za ta iya ba da taimako kan aikin raya kasar Senegal.

A ran 11 ga wata da safe, tare da ministan harkokin al'adun kasar Senegal, Mr. Wang ya ziyarci babban dakin wasan kwaikwayo na kasar, wanda kasar Sin ta taimaka wajen gina shi, mista Wang Yi ya bayyana cewa, wannan taimako ya nuna alfanun dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

A tsawon kwanaki shida da suka gabata, daga ranar 6 zuwa rana 11 ga wata, Mr. Wang ya ziyarci kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara guda hudu da suka hada da kasashen Habasha, Djibouti, Ghana, da kuma Segenal.

Yawancin kafofin watsa labarai na kasashen Afirka sun nuna yabo sosai da ziyarar ministan harkokin wajen kasar Sin a nahiyar Afrika. Ban da wannan kuma, kafofin watsa labarai sun mai da hankali sosai kan ayyuka da taimako da kasar Sin za ta samar a wadannan kasashe a nan gaba, da suka hada da gina manyan hanyoyin mota a kasar Senegal da dai sauransu, lamarin dake bayyana fatan alheri na al'ummomin kasashen kan hadin gwiwa tare da kasar Sin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China