in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar ministan harkokin wajen Sin a kasashen Afirka guda hudu ta inganta manufar diflomasiyya ta Sin
2014-01-13 20:21:48 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ziyarci kasashen Habasha, Djibouti, Ghana, da kuma Segenal daga ranar 6 zuwa 11 ga wata, wasu masana suna ganin cewa, ziyararsa a wadannan kasashe hudu ta karfafa fahimta da hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, tare da inganta manufar diflomasiyar kasar Sin.

Shugaban cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa na kasar Sin Qu Xing ya bayyana cewa, ya kamata a ci gaba da mai da hankali kan raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, kuma ya kamata kasar Sin ta cika dukkan alkawuran da ta yi wa kasashen Afirka.

Bugu da kari, yayin ziyararsa a kasashen Afirka, Mr. Wang ya gana da wakilan bangarorin dake adawa da juna na ricikin kasar Sudan ta Kudu a birnin Addis Ababa, inda ya bayyana cewa, a matsayin abokiyar kasar Sudan ta Kudu, kasar Sin tana son ba da taimako wajen ciyar da shawarwarin zaman lafiya dake tsakanin bangarorin biyu da rikicin ya shafa gaba.

Wata masaniya a sashen nazarin Afirka da yammacin Asiya na cibiyar nazarin ilmin zamantakewar al'umma ta kasar Sin, He Wenping ta bayyana cewa, aikin shiga tsakani da ministan harkokin wajen kasar Sin ya yi, yana wakiltar manufa da matsayin kasar Sin ne kan harkokin kasashen Afirka, kuma zai ba da taimako ga zaman lafiya da kuma tsaron nahiyar Afirka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China