in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Ghana ya gana da ministan harkokin wajen Sin
2014-01-10 09:17:22 cri

Ranar Alhamis 9 ga wata ne, a fadar shugaban kasar Ghana dake Accra, babban birnin kasar, shugaban kasar John Dramani Mahama ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Mista Wang Yi da a halin yanzu ke ziyara a kasar, inda bangarorin biyu suka cimma matsaya cewa, za su himmatu wajen karfafa hadin-gwiwa tsakaninsu.

Ministan harkokin wajen kasar Sin Mista Wang Yi ya isa birnin Accra ne a ranar 8 ga wata, inda a wannan rana ya yi shawarwari tare da takwararsa ta kasar Madam Hannah Tetteh. Sa'an nan a ranar 9 ga wata, ya ziyarci wurin tunawa da shugaban kasar Ghana na farko, marigayi Dr. Kwame Nkrumah dake birnin Accra. Bayan haka, Mista Wang ya je fadar shugaban kasa don ganawa da shugaba John Dramani Mahama.

Mahama ya ce, kasar Sin ta jima tana hadin-gwiwa tare da kasashe maso tasowa, musamman ma bayar da dimbin taimako ga kasashen Afirka, domin taimaka musu wajen samun farfadowa.

Mahama ya ce, "Zurfafa yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje da kasar Sin take yi a halin yanzu, ba ma kawai ya sa Sin ta samu ci gaba ba, har ma yana baiwa kasashe maso tasowa kwarin-gwiwa sosai. Kasar Ghana ta amfana da yawa daga tallafin da kasar Sin ta samar mata, kuma tana fatan kara dankon zumunci da hadin-gwiwa tare da kasar Sin."

A nasa bangaren, Mista Wang Yi ya ce, tsofaffin shugabannin kasashen Sin da Ghana ne suka kulla dadaddiyar dangantakar abokantaka tsakaninsu, wannan tamkar wata babbar dukiya ce gare su. Sa'an nan akwai fannonin tattalin arziki da dama wadanda kasashen biyu ke iya yin hadin-gwiwa tsakaninsu. Dadadden zumunci gami da fannonin hadin gwiwa da dama tsakanin Sin da Ghana sun sa kasashen biyu suna da hulda mai kyau.

Mista Wang ya ce, "Idan muka hada dadadden zumuncin da kuma fannonin hadin-gwiwa tare, wato a yi kokarin fadada hadin-gwiwa ta hanyar karfafa wannan dadadden zumunci, da kuma saka sabbin abubuwa cikin wannan zumunci ta hanyar habaka fannonin hadin-gwiwa, to hakika za'a kara samun dangantakar abokantaka mai dorewa tsakanin Sin da Ghana."

A ranar 9 ga wata da dare ne ministan harkokin wajen kasar Sin Mista Wang Yi ya tashi daga kasar Ghana, inda zai fara wata ziyarar aiki a kasar Senegal.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China