Mr Wang ya fadi hakan ne bayan da ya gana da takwaransa na kasar Senegal mista Mankeur Ndiaye, yana mai bayanin cewa Shugaban kasar Sin Xi Jinping ne ya bayyana wannan manufar na kokarin nuna adalci lokacin da ya ziyarci nahiyar Afirka a bara. Yace Ma'anar manufar ita ce, kasar Sin za ta mai da hankali kan nuna adalci a kokarinta na mu'amala da kasashen Afirka, inda za ta yi kokarin kulla abokantaka, da tabbatar da daidaituwa, tare da cika alkawuran da ta dauka, haka zalika za ta yi kokarin kare hakkin kasashen Afirka da taimakawa biyan bukatunsu.
Ban da haka kuma, a cewar mista Wang, manufar ta shafi alkawarin da kasar Sin ta dauka na tabbatar da moriyar juna yayin da take hulda da kasashen nahiyar Afirka, inda kasar Sin za ta magance hanyar da Turawa 'yan mulkin mallaka suka bi ta kokarin kwatan albarkatun kasa daga Afirka don biyan bukatansu kawai.
Maimakon haka yace,kasar Sin za ta yi kokari tare da kawayenta dake Afirka don tabbatar da ci gaba da walwala a bangarorin 2. Ban da haka kuma, yayin da Sin da kasashen Afirka suke hadin kai,kasar Sin za ta kara mai da hankali kan bukatun kasashen Afirka. Kuma idan akwai bukata, za ta iya sadaukarwa da moriyar kanta don tabbatar da nuna adalci ga kasashen Afirka. (Bello Wang)