Al-Abad ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, yana mai cewa harin sama da sojojin kasar Amurka suka kai ya taimakawa dakarun kasar ta Iraki wajen fatattakar mayakan kungiyar ta ISIS, sai dai a cewar sa ba zasu bukaci taimakon sojojin kasa na kasashen waje a wannan yaki ba. Hasalima dai Iraqin ba za ta amince da shigarsu ba.
Wadannan kalamai na Al-Abad dai tamkar martani ne ga tsokacin da wani babban hafsan sojojin kasar Amurka Martin Dempsey ya yi, cewa mai yiwuwa ne a bukaci tura sojojin kasa na Amurka zuwa Iraki, don yaki da dakarun ISIS.
A ranar 17 ga watan nan ne dai shugaba Barack Obama na Amurka, ya sake alkawarta cewa kasarsa ba za ta tura sojojin kasa ba domin yaki da mayakan kungiyar ta ISIS masu da'awar kafa daular Islama a wasu yankunan Iraqi da Syria. (Zainab)