Kakakin ma'aikatar harkokin tsaron kasar Amurka John Kirby ya bayar da sanarwa a rubuce a daren jiya, inda ya tabbatar da cewa, sojojin kasar Amurka da sojojin kasashen kawancenta sun fara kai hari ta sama kan kungiyar ISIS dake kasar Syria.
Wannan ne karo na farko da kasar Amurka ta kai hari ta sama ka yankunan kungiyar ISIS a kasar Syria bayan harin da take kaiwa kan kungiyar ISIS dake kasar Iraki tun cikin watan Agusta. Kafofin watsa labaru na kasar Amurka sun tsamo maganar jami'in ma'aikatar harkokin tsaron kasar cewa, wasu kasashen Larabawa kamar su Saudiyya, Jordan, Hadaddiyar daular Larabawa sun sa hannun aikin kai harin sama a kasar Syria, lamarin da ya lalata gine-ginen kungiyar ISIS kimanin 20, ciki har da ginin cibiyar kungiyar ISIS. (Zainab)