Obama da Ban Ki-moon sun tattauna game da kafa kawancen kasa da kasa wajen yaki da kungiyar ISIS
Fadar shugaban kasar Amurka ta White House ta fidda wata sanarwa dake cewa, shugaban kasar Barack Obama ya zanta da babban magatakardar MDD Ban Ki-moon da firaministan kasar Australia Tony Abbott ta wayar tarho, inda suka tattauna game da kudurin kafa kawancen kasa da kasa domin yaki da kungiyar ISIS mai rajin kafa kasar Musulunci.
Cikin sanarwar, fadar shugaban kasar Amurka ta bayyana cewa, Obama da Ban Ki-moon sun yi imani cewa, akwai bukatar kafa wani kawance na kasa da kasa, domin yaki da kungiyar ta ISIS, kana sun yi alkawarin ci gaba da bada gudummawar jin kai, ga fararen hula na kasar Iraki da ke fuskantar barazanar kungiyar ta ISIS. (Zainab)