Da yake jawabi ga taron jin ra'ayin jama'a da kwamitin aikin soja na majalisar dattijan kasar Amurka ya gudanar game da yaki da kungiyar ta ISIS, Dempsey ya bayyana cewa kafa kawance shi ne hanya mafi dacewa wajen yaki da kungiyar ta ISIS. Amma idan hakan ya ci tura, ISIS din na iya barazana ga kasar Amurka, wanda bisa wannan dalili zai shawarci shugaba Obama, ya duba yiwuwar amfani da sojojin kasa a yakin da ake yi da kungiyar mai da'awar kafa daular Islama.
Sai dai a daya hannun masu adawa da yaki a kasar ta Amurka na nuna adawarsu ga wannan taro na jin ra'ayin jama'a. (Zainab)