in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka da abokan kawancen Larabawa sun amince da dakusar da ba da kudi ga ISIS
2014-09-12 14:30:25 cri

Kasar Amurka da sauran abokan huldarta daga kasashen Larabawa, sun amince a wani taro cewar, za su dunkule karfi wuri guda, domin kaddamar da wani kamfe na murkushe kafuwar wata sabuwar kungiya ta Jihadi.

A cikin wani bayanin bayan taro na hadin gwiwa, a karshen tattaunawar da suka yi a Saudi Arabia, kasashen sun kuma amince da su dakusar da ba da kudi ga mayakan kungiyar kasar ta Musulunci IS, tare da daukar mataki na taimakawa mutanen da kungiyar kasar Musuluncin suka zalunta domin su kara gina wata sabuwar rayuwa.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya jaddada cewar, akwai gagarumar bukata ga kasashen Larabawa da su dauki mataki na murkushe kasar Musulunci, ya ce, Amurka na kokarin hada kawunan kasashen duniya domin yaki da wannan gagarumar barazana ta ISIS.

Kamfanin dillancni labarai na Saudi Arabia ya ce, John Kerry da wasu jami'an kasar ta Amurka suna ci gaba da kaddamar da shirin yaki da kungiyar kasar ta Musulunci kamar yadda Obama ya bayyana a ranar Laraba, da zimmar wargaza kungiyar.

Taron wanda aka yi a Jeddah a kasar Saudi Arabia ya samu halarcin ministocin harkokin waje na Saudi Arabia, Amurka, Masar, Iraq, Jordan, Lebanon da kuma kasashen Larabawa guda shida dake yankin Gulf.

Ana sa rai cewar, Kerry zai gana da magatakardan hadaddiyar kungiyar Larabawa Dr. Nabil Al-Arabi a gobe Asabar domin ci gaba da tattaunawa a kan al'amuran da suka shafi yankin. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China