in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ISIS ta gabatar da bidiyon kisan dan Birtaniya da ta yi
2014-09-14 16:58:19 cri

Kungiyar masu da'awar kafa daular musulunci a Iraqi da Sham ko ISIS a takaice, ta fidda wani faifan bidiyo a kan yanar gizo, wanda ya nuna kisan David Haines wani dan Birtaniya da take tsare da shi.

Mayakan ISIS din dai sun ce hakan martani ne ga gwamnatin Birtaniya, na alkawarta taimakawa Amurka wajen yaki da kungiyar.

Dadin dadawa, faifan bidiyon ya nuna wani mayakin kungiyar lullube da fuska, na cewa ISIS za ta kashe wani karin dan kasar ta Birtaniya, muddin firaminista David Cameron bai sauya ra'ayi game da taimakawa yaki da kungiyar ba.

Shi dai Haines mai shekaru 44 a duniya, an yi garkuwa da shi ne a bara ya yin da yake aiki da wata hukumar ba da taimako ta kasar Faransa.

Sai dai a nasu bangare kasashen Amurka da Birtaniya, sun mai da martani game da hakan nan da nan, inda firaminista Cameron ya fidda wata sanarwa dake cewa, kisan dan kasar tasa da ISIS ta yi rashin imani ne, kuma gwamnatinsa za ta yi iyakacin kokarin ganin an gurfanar da masu hannu cikin wannan ta'asa gaban kuliya koda kuwa hakan zai dauki lokaci mai tsaho.

Shi kuwa shugaba Barack Obama na Amurka ya fitar da wata sanarawa dake suka da kakkausar murya, tare da yin Allah wadai da karfin tuwo, irin wadanda mayakan na ISIS suka nuna kan Haines. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China