in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan Iraki na yin nazari kan bidiyon da ake tukumar shugaban kungiyar ISIS a ciki
2014-07-07 10:15:46 cri

Kakakin sojojin kasar Iraki ya bayyana cewa, yanzu mahukuntan kasar ta Iraki na yin nazari ta fuskar fasaha kan bidiyon da kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta ISIS ta fitar a kwanan nan, a kokarin tabbatar da cewa, mutumin da ke cikin bidiyon shi ne shugaban kungiyar wato Abu Bakr al- Baghdadi ko a'a.

Idan an tabbatar da cewa, Baghdadi ne, to wannan shi ne karo na farko da ya nuna kansa cikin bidiyo.

Kungiyar ISIS wani tsohon reshe ne na kungiyar ta'addanci ta AL-Qaeda da ke kasar Iraki, wadda ke mallakar wasu yankunan dake arewaci da kuma gabashin kasar Sham. Tun bayan farkon watan Yuni na bana kuma, kungiyar ta kwace ikon wasu yankunan da ke arewacin kasar Iraki.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China