Sanarwar ta bayyana cewa, wannan mugun aiki ya yi nuni da cewa, kungiyar ISIS na saba wa ka'idojin kasa da kasa, tare da ci gaba da gudanar da ayyukan ta'addanci. Kaza lika sanarwar ta yi tir da ayyukan ta'addanci da wannan kungiyar ke aiwatarwa, wadda ke da alaka da kungiyar al-Qaida.
Ban da wannan, sanarwar ta kara da cewa EU za ta ci gaba da goyon bayan kasashen duniya wajen yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda, da kuma kokari tare da sauran kasashe wajen kame tare gurfanar da 'yan ta'adda gaban kuliya.
A ranar Asabar din data gabata ne dai kungiyar ta ISIS ta fidda wani faifan bidiyo a shafin internet, wanda ya nuna kisan dan Britaniyan mai suna David Haines, wanda kungiyar ta kame a kasar Syria a shekarar da ta gabata. Kungiyar ta dauki wannan mataki ne don mayar da martani ga gwamnatin Britaniya, game da alkawarin taimakawa kasar Amurka wajen yaki da kungiyar.
A wani ci gaban kuma kwamitin sulhun MDD ya fidda wata sanarwa a jiya Lahadi, da ita ma ke Allah wadai da kisan David Haines. Sanarwar ta kuma ce ya zama wajibi a ci gaba da yakin da ake yi har sai an kai ga murkushe kungiyar ta ISIS. (Zainab)