Sanarwar ta ce, wadannan kasashe sun amince da hana dakaru masu tsattsauran ra'ayi da su shiga Syria ko Irak daga kasashen makwabta, da yaki da aikin zuba jari ga kungiyar ISIS da sauran kungiyoyin ta'addanci, a kokarin cafke su bisa dokoki.
Dadin dadawa, kasashen sun amince da ba da taimakon jin kai ga yankunan dake fama da ayyukan ta'addanci, domin ba da taimako wajen samun farfadowa, da nuna goyon baya ga kasashen dake yin gwagwarmaya da kungiyoyin ta'addanci.(Fatima)