Wani gidan talibijin mallakar kasar ta Iran ya rawaito Abdollahian na cewa, Iran ba ta da sha'awar halartar irin wannan taron da ya zabi wasu kasashe domin halartarsa bisa son rai, kuwa a cewarsa taron zai kasance tamkar wani wasan kwaikwayo. Mr. Abdollahian ya kara da cewa, Iran ta fi sha'awar sanya hannu cikin wasu sahihan ayyuka na yaki da ta'addanci a shiyyar gabas ta tsakiya, da ma ragowar sassan duniya baki daya.
Kaza lika, Abdollahian ya jaddada cewa, Iran kasar ce da ke kan gaba wajen daukar matakan taimakawa kasar Iraki wajen yaki da ta'addanci. A nan gaba kuma, za ta ci gaba da marawa Iraki da kasar Siriya baya a wannan fanni.
Wannan tsokaci dai na mahukuntan kasar Iran, na zuwa ne bayan da kasar Amurka ta sanar da kafa kawance tare da wasu kasashen Larabawa goma, domin yaki da kungiyar ISIS, matakin da ya sanya Iran din bayyanawa duniya cewa, ba za ta shiga kawance da Amurka a wannan fanni ba.(Kande Gao)