Yayin ganawar ta tsawon kimanin awoyi biyu, shugaba Obama ya bayyana cewa idan akwai bukata, yana da ikon daukar matakan soji kan dakarun kungiyar ta ISIS. Wato dai ba shi da bukatar amincewar majalisar dokokin kasar game da hakan.
Kaza lika Obama yana fatan majalisar dokokin kasar za ta ci gaba da daukar matakai wadanda za su taimaka wa matakan da yake dauka, kana su shaidawa duniya cewa sassa daban daban na kasar Amurka na daukar matsayin bai daya kan wannan lamari.
Rahotanni sun nuna cewa shugaba Obama zai gabatar da wani jawabi ta kafar telebijin a daren yau Laraba, gabanin cika shekaru 13 da harin ta'addancin nan na 11 ga watan Satumba. Ana kuma sa ran cikin jawabin na sa zai sanar da manufofin gwamnatin sa game da yaki da kungiyar ta ISIS.
Kaso biyu bisa uku na Amurkawa dai na da ra'ayin cewa, kungiyar ISIS na barazana ga kasar Amurka, suna kuma goyon bayan gwamnatin kasar a fannin daukar matakan yaki da kungiyar. (Zainab)