in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta kafa wata tawagar musamman domin shawo kan cutar Ebola
2014-09-20 16:41:58 cri

Babban magatakardan MDD Mr Ban Ki-Moon ta bakin kakakinta ya ba da sanarwar kafa wata tawagar musamman domin shawo kan cutar Ebola, tare kuma da ba da umurnin ga rukunin share fage da ya isa yammacin Afrika a ran 22 ga wata.

Sanarwar kuma ta nuna cewa, bayan kwamitin sulhu na MDD ya kira wani taron cikin gaggawa a ran 18 ga wata, kuma taron MDD ya zartas da wasu kudurori dake da nasaba da cutar Ebola, Mr. Ban ya kafa wannan tawaga ta musamman, wadda za ta samar da tsarin aiki da tsaida manufar da za a cimmawa gaba daya, da tabbatar da daukar mataki mai amfani cikin lokaci ta yadda za a kawo karshen wannan cutar, tare da ba da jiyya ga wadanda suka kamu da cutar da dai sauransu ayyuka dake da nasaba da wannan batu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China