Wannan jami'i na WFP wanda ya bayyana hakan a nan birnin Beijing, a 'yan kwanakin baya ya kara da cewa bisa kididdigar da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta fitar, ya zuwa ranar 12 ga watan nan, yawan mutanen da suka rasu sakamakon kamuwa da cutar Ebola ya wuce 2400, yayin da jimillar wadanda suka kamu da cutar ya kai mutane kusan 4800.
Tuni dai hukumar WFP ta gabatar da wani rahoto dake cewa domin yaki da yaduwar cutar Ebola, ta samar da abinci ga mutane kimanin miliyan 1 da dubu 300, dake zaune a yankunan killace mutane dake kasashen Guinea, da Liberia da Saliyo.
Game da hakan wakilin reshen hukumar dake kasar Sin Huang Ansheng, ya bayyana cewa ana iya amfani da abincin da hukumar ta WFP ta samar har na tsawon kwanaki 90, wanda hakan zai iya biyan bukatun abinci na jama'a, da rage zirga-zirgar mutane, kuma hakan na iya taimakawa hana yaduwar cutar. (Zainab)