Rundunar sojojin saman kasar Ghana ta fara isar da taimakon da ya hada da kusan ton 100 na kayayyakin ceto da na abinci, zuwa Liberiya, Saliyo da Guinea, kasashen da su fi fama da cutar Ebola. Kayayyakin da suka hada da buhuhuwan shimkafa dubu uku, katunan man dafuwa dari uku, katunan madara dari uku da kwalayen madarar sha ta kwakwa dari uku.
Kasar Ghana ta ba da wannan taimako a rana guda da ziyarar shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, kuma shugaban kungiyar ECOWAS a wannan karon ya kai a kasashen da cutar Ebola ta shafa. Taimakon kuma ya shafi mutanen dake samun kulawa a wasu asibitoci da kuma maras lafiya da aka killace dake samun jinya a wasu cibiyoyi. (Maman Ada)