Kudurin ya bayyana cewa, cutar Ebola tana kawo illa ga zaman lafiyar kasashen Liberia, Guinea, Saliyo da Nijeriya, idan har aka kasa dakatar da yaduwarta, watakila ma wannan annoba zata iyar haddasa barkewar rikice-rikicen cikin gida, tsanantar halin tsaro da na siyasa a wadannan kasashen.
A gun taron, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, za a kafa wata tawagar musamman don samar da guzuri da taimako wajen yaki da cutar Ebola.
Bisa bukatun kayayyaki da MDD take dasu da aka gabatar a wannan mako, an ce ana bukatar gudummawar da ta kai yawan kimanin dala biliyan daya a watanni shida masu zuwa.
Ban da wannan kuma, Ban Ki-moon ya nuna godiya ga kasashen Sin da Cuba da Canada kan rawar a zo a gani da suka taka wajen taimakawa kokarin yaki da cutar Ebola. (Zainab)