in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen tsakiyar Afrika za su tattara kudade domin ragakafin Ebola
2014-09-19 10:26:07 cri

Ministocin kiwon lafiya na kasashen mambobin gamayyar tattalin arziki da kudi ta tsakiyar Afrika (CEMAC), a yayin wani taronsu na ranar Alhamis a Brazzaville na kasar Congo, sun jaddada wajabcin tattara kudade domin tallafawa ayyukan rigakafin cutar Ebola.

Ministocin kasashen shida da suka hada da Kamaru, Afrika ta Tsakiya, Congo, Gabon, Guinee-Equatoriale da Chadi sun amince da wani shirin gaggawa na shiyyar domin yakar annobar Ebola, da kwararrun kasashen shiyyar suka kirkiro a ranakun Talata da Laraba. Haka kuma sun bukaci aiwatar cikin gaggawa da wannan shirin a shiyyar CEMAC, dake bukatar a cewarsu, tattara makudan kudade. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China