in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen tsakiyar Afrika na shirya shirin hadin gwiwa na rigakafin cutar Ebola
2014-09-18 10:55:21 cri

Kwararrun kasashe mambobi shida na gamayyar tattalin arziki da kudi ta tsakiyar Afrika (CEMAC) sun cimma a ranar Laraba, a birnin Brazzaville na kasar Congo, da wani shirin gaggawa domin fuskantar cutar Ebola. Wannan shirin, za'a gabatar da shi ga ministocin kiwon lafiya na kasashen shida, wadanda suka hada da Kamaru, Congo, Gabon, Guinee-Equatoriale, Afrika ta Tsakiya da Chadi yayin wani taro a ranar Alhamis a hedkwatar kasar Congo.

Kuma shirin ya shafi musamman ma ayyukan dake da nasaba da kan iyakoki, hadin kan al'ummomin shiyyar, da fannin sadarwa, sanya ido kan cututtuka masu yaduwa, da ma kokarin daukar nauyin wasu nau'o'in cututtuka, da kuma kulawa da maras lafiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China