Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya bayyana a ranar Talata cewa, a yanzu babu wani nau'in cutar Ebola a wannan kasa.
A yanzu, babu wani nau'in cutar Ebola a Najeriya, babu wani mutumin da ya kamu da wannan cuta a yanzu, kana yawancin mutanen da suka kamu sun warke daga cutar.
Bisa mutane goma sha tara da suka kamu da cutar, mun rasa mutane bakwai yayin da sauran suka samu lafiya, ko da yake har yanzu wasu daga cikinsu ana sanya ido kansu, in ji shugaba Jonathan a birnin Abuja, hedkwatar kasar.
Shugaba Jonathan ya kara da cewa, ci gaba da rufe makarantu zai isar da wani sakon maras kyau ga gamayyar kasa da kasa game da matsalar Ebola a Najeriya. (Maman Ada)