Shugaban gudanarwa na ba da taimako ga ayyukan tunkarar cutar Ebola na kungiyar tarayyar Afrika AU a Afrika ta yamma, Manjo janar Julius F. Oketta, ya ce, kungiyar ta AU za ta tura da kwararrun likitoci da nas-nas zuwa kasar Liberia da zimmar samar da ma'aikatan lafiya kwararru, wadanda za su taimaka wajen kula da lafiyar wadanda suka kamu da cutar Ebola.
A yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai a Monrovia, fadar gwamnatin kasar ta Liberia, Oketta ya ce, matakin da AU ta dauka na da zimmar marawa matakan taimako da kasashen duniya ke yi a yakin da ake yi da cutar Ebola a kasar.
Ya ce, za'a tura ma'aikatan lafiya a karkashin rukunoni 2, a inda rukuni na farko wanda ke kunshi ma'aikatan lafiya 100, zai isa Liberia ya fara aiki har tsawon makonni shida, daga baya kuma sai rukuni na biyu ya maye gurbin farko a karkashin kokarin da ake na takawa cutar Ebola birki. (Suwaiba)