in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matakan hana tafiya sun kara kawo matsala ga yaki da Ebola, in ji WHO
2014-09-18 10:26:12 cri

Matakan hana tafiye-tafiye zuwa kasashen yammacin Afrika dake fama da cutar Ebola sun lalata kokarin da ake yi wajen yaki da annobar, in ji wani jami'in hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO).

Darektan shiyyar Afrika na hukumar WHO, Luis Gomes Sambo, ya bayyana damuwa kan yadda kasashe suka yi adawa da matakan kiwon lafiya na kasa da kasa domin gitta wasu sharudan hana tafiye-tafiye zuwa muhimman yankunan da cutar Ebola ta fi kamari.

Matakan hana bulaguro zuwa kasashen da suke fama da cutar Ebola sun dakushe aikin tura taimakon jin kai na gaggawa, har da ma'aikatan kiwon lafiya da kayayyakin bukatun yau da kullum, in ji mista Sambo a yayin wani zaman taro a birnin Nairobi tare da ministocin kiwon lafiya na shiyyar kan hanyoyin da za'a dauka wajen yaki da cutar Ebola. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China