in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan ba da gudunmawa wajen tinkarar cutar Ebola
2014-09-19 20:32:56 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Mr Hong Lei ya bayyana yayin zantawa da manema labaru a yau Juma'a 19 ga wata a nan birnin Beijing cewa, gwamnatin kasar Sin za ta baiwa kasashen yammacin Afrika karin tallafin kudi na Yuan miliyan 200 don tinkarar cutar Ebola, tare da fatan gudummawar da za ta bayar za ta taimaka wajen shawo kan cutar cikin hanzari

Mr. Hong ya yi bayyani cewa, tun barkewar wannan cuta a yammacin Afrika, gwamnatin kasar Sin da jama'arta sun nuna damuwa kan halin da al'umma kasashen da cutar ta bulla suka shiga, kuma nan da nan ta ba da taimakon kudi da na kayayyaki da hatsi.Ban da haka kuma, Sin ta tura kwararrun aiki kiwon lafiya da yawansu ya kai 174 zuwa wadannan kasashe dake fama da cutar.

Ya zuwa yanzu, cutar tana ci gaba da yaduwa a yammacin Afrika, a cewarsa, Sin na fatan kara hadin gwiwa da kasashen duniya, don ba da gudunmawar da ta dace ta yadda za a shawo kan cutar nan da nan.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China