in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan Najeriya sun yi kira ga malamai da su koma makaranta
2014-09-18 10:17:07 cri

Shugaba Goodluck Jonathan na tarayyar Najeriya, ya ce, a halin yanzu babu wani 'dan kasar da aka tabbatar yana dauke da cutar Ebola, kuma gwamnatinsa na ci gaba da daukar matakan tabbatar da hana sake bullar cutar.

Kalaman shugaban kasar dai na zuwa ne gabar da kungiyar malaman makarantar kasar NUT, ke barazanar shiga yajin aiki domin nuna rashin gamsuwa da umarnin mahukuntan kasar na sake bude makaratu a ranar 22 ga watan Satumbar nan.

Game da hakan, shugaba Jonathan ya bukaci kungiyar ta NUT, da sauran kungiyoyin kwadagon kasar da su yi watsi da duk wani shakku game da cutar Ebola, su kuma amince da kudurin gwamnatin na sake bude makarantun.

Ya ce, an samar da kayan binciken lafiya a dukkanin manyan filayen jiragen saman kasar, domin kare shigar wani da cutar ta Ebola cikin kasar.

Kaza lika shugaban Najeriyar ya ce, kin amincewa da sake bude makarantun, na iya sanya kasashen waje su rika kallon duk wani 'dan Najeriya da zai shiga kasashensu tamkar yana dauke da cutar ta Ebola. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China