Babban bankin duniya (BM) ya amince a ranar Talata da wani taimakon dalar Amurka miliyan 105 domin magance matsalar cutar Ebola zuwa ga wasu kasashe uku dake yammacin nahiyar Afrika, inda wannan annoba ta janyo mutuwar mutane fiye da dubu biyu da dari hudu tun farkon wannan shekarar.
Taimakon dai ya shafi samar da kudade kan kokarin da ake na hana yaduwar cutar Ebola na kan hanyar isa kasashen Guinea, Liberiya da Saliyo. (Maman Ada)