Mr. Hong ya bayyana hakan a gun taron manema labaru, inda ya ce cewa, a kokarin kara nuna goyon baya ga wasu kasashen Afirka a fannin shawo kan cutar Ebola, da la'akari da bukatar gwamnatin Saliyo, da kuma amsa kiran kungiyar hukumar WHO na neman goyon baya kan yadda za a shawo kan cutar Ebola a Afirka, a jiya Talata 16 ga wata, gwamnatin Sin ta tura rukunin masu bincike daga cibiyar shawo kan cututtuka ta Sin mai kunshe da mutane 59 zuwa Saliyo, domin taimakawa kasar wajen yin bincike kan cutar Ebola, da zummar kara karfin Saliyo a fannin yin bincike. Wannan rukuni zai fara aiki a asibitin sada zumunci tsakanin Sin da Saliyo da Sin ta ba da taimako wajen kafa shi.
Ban da haka, mista Hong ya kara da cewa, Sin ta dade tanana ta kokarin shawo kan cutar Ebola tare da sauran kasashen duniya. Kuma ta ba da kayayyakin agaji ga kasashen Guinea, Liberiya, Saliyo, da kuma Guinea Bissau cikin sauri. Rukunonin likitoci da Sin ta tura zuwa kasashen waje sun aiwatara ci gaba da da ayyukansu yadda ya kamata duk da barazanar da suke fuskanta, baki daya likitoci 115 ne suka suke gudanar da ayyukan shawo kan cutar Ebola a wurin. A wannan karo, kasar ta Ssin ta kara tura ma'aikata 59, adadin dadon haka, yawan likitocin kasar Sin da ke wurin ya karu ya yanzu ya kai zuwa 174. Wannan ya bayyana dankon zumunci dake tsakanin Sin da kasashen Afirka, da kuma ra'ayin jin kai na jama'ar Sin.(Fatima)