Rukunin likitocin dai ya hada da likitoci 10 daga asibitin Youyi, wadanda za su gudanar da ayyukansu na tsawon shekaru biyu a asabitin sada zumunci tsakanin Sin da Guinea dake birnin na Conakry.
Wannan dai rukunin likitoci zai kula da marasa lafiya, tare da ba da kariya bisa kimiyya, bayan da ya samu amincewar kwamitin kiwon lafiya da kayyade iyali na kasar Sin, da ofishin jakadancin Sin a kasar Guinea.
A daya bangaren kuma rukunin masanan da aka tura ya kunshi kwararru uku, daga cibiyar shawo kan yaduwar cututtuka ta birnin Beijing, da asibitin Ditan, da kuma asibitin Xiehe. Za kuma su kula da kamfanonin Sin dake kasar, da rukunin masu aikin jiyya a fannin yaki da cutar Ebola.
Tuni dai hukumar lafiya ta duniya WHO, ta bayyana cutar Ebola a matsayin annobar da ke bukatar a daukar ma ta matakan gaggawa, wadda duniya ta mai da hankali kwarai game da ita.
Har wa yau WHOn ta shawarci kasashen dake fama da wannan cuta, da su aiwatar da dokar ta baci game da matakan yaki da ita.
Game da hakan shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya ayyana dokar ta baci game da yunkurin da gwamnatin sa ke yi, don gane da shawo kan wannan cuta. Wanda hakan ya nuna cewa daukacin kasashen yammacin Afirka hudu dake fama da cutar ta Ebola sun shiga halin kota kwana game da magance yaduwar ta.(Fatima)