Wata sanarwa da ma'aikatar cinikayya ta Sin ta bayar, ta ce tallafin zai hada da abinci, kayayyakin hana yaduwar cututtuka, kayayyakin rigakafin ko-ta-kwana da tallafin jari.
Bugu da kari kasar ta Sin za ta karfafa wani hadin gwiwar kiwon lafiya da kasashen Afirka na dogon lokaci, don agaza musu wajen inganta karfin hanyoyinsu na kare yaduwar cututtuka da kuma inganta tsarinsu na kiwon lafiya.
Ko da a watan da ya gabata, Sin ta baiwa kasashen na Afirka tallafin jin kai na Yuan miliyan 30.
A cewar hukumar lafiya ta duniya mutane 4,268 ne suka kamu da cutar ta Ebola yayin da mutane 2,288 suka mutu a kasashen Guinea, Liberia, Saliyo da Najeriya sanadiyar cutar. (Ibrahim)