Tawagar dai a cewar wannan ofishi na kunshe ne da kwararru 59 daga cibiyar rigakafi da yaki da cututtuka ta kasar Sin. Za kuma ta maida hankali wajen gudanar da ayyukan bincike kan cutar ta Ebola tare da taimakawa kasar Saliyon wajen inganta karfinta na bincike kan cututtuka.
Har ila yau an ce tawagar ta hada da kwararru a fannonin bincike, da ilimin yaduwar cututtuka, da fannin jinya da dai sauransu. Kana rukunin zai yi aiki a asibitin sada zumunta na Sin da Saliyo, da nufin taimakawa kasar wajen sa ido kan cutar Ebola da dai sauransu.
Tun bayan barkewar cutar Ebola a wasu kasashen yammacin Afirka a wannan karo, an tura likitoci 115 daga kasar Sin domin shiga aikin yaki da cutar a kasashen da ta fi yaduwa, ciki hadda likitoci 88 masu aiki na tsahon lokaci, da masana 27 masu gudanar da aikin wucin gadi.
A kuma wannan karo, Sin ta tura karin likitoci 59, matakin da ya sanya jimillar likitocin kaiwa 174. (Zainab)