Sashen nazarin kananan halittu da cututtuka masu yaduwa na kwalejin kimiyyar likitoci na sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin ta shafe tsawon shekaru biyar ta kirkiro wani magani da ake kira jk-05 don kawar da cutar Ebola. A kwanakin baya, masanan sashen harkokin kiwon lafiya ta sojojin sun yi bincike da kuma amince da shi a matsayin maganin musamman ga sojojin. Wannan nau'in magani tare da maganin bincike kan cutar Ebola da aka amince da samar da su a kwanakin baya sun kasance muhimmin abin ga kasar Sin wajen yaki da cutar Ebola.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, wannan ne karon farko da kasar Sin ta amince da maganin kawar da cutar Ebola. (Zainab)