in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya sanar da sake baiwa kasashen duniya tallafi wajen yaki da Ebola
2014-09-18 19:03:33 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda ke ziyarar aiki a kasar Indiya ya sanar a yau Alhamis 18 ga wata a birnin New Delhi cewa, gwamnatin kasar ta Sin za ta baiwa kasashen duniya karin taimako wajen yaki da cutar Ebola.

Mr. Xi ya nuna cewa, domin taimaka wa kasashen Laberiya, Saliyo da Guinea da sauran kasashe dake kewayen wadannan kasashen dake fama da Ebola wajen kara karfin tinkarar cuta, tare kuma da nuna goyon baya ga kungiyoyin kasa da kasa su taka rawar jagora wajen yaki da wannan cuta, gwamnatin kasar Sin ta yanke shawarar bayar da karin tallafi na Yuan miliyan 200 da hatsi da kayayyakin tallafi ga wadannan kasashen uku da cutar ta ritsa da su.

Bugu da kari ta kuma baiwa hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO da kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU kowacensu tallafin kudi dala miliyan biyu.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China