A yayin da kakakin babban magatakardan MDD Stephane Dujarric ya gabatar da wannan sanarwa, ya ce, a halin yanzu, domin yaki da cutar Ebola, kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU tana kokarin tura likitoci zuwa kasashen dake fama da cutar, haka kuma, ana ci gaba da samun taimakon kudade, kayayyakin agaji da masanan kiwon lafiya daga kasa da kasa, kungiyoyi da kuma kamfanoni masu zaman kansu suka samar.
Bugu da kari, cikin sanarwar, Mr. Ban ya nuna maraba ga kasashen Burtaniya da Amurka da suka tura masanan kiwon lafiya zuwa yammacin kasashen Afirka, da kuma gina cibiyar agaji a kasashen, ya kuma yi kira ga karin hukumomin kasa da kasa da su dauki matakai cikin sauri don samar wa kasashen dake fama da cutar Ebola taimako yadda ya kamata.
A sa'i daya kuma, Mr. Ban ya yi kira ga kasashen da abin ya shafa da kada su rufe iyakokinsu da kasashen Guinea, Saliyo da dai sauran kasashen da cutar Ebola ta shafa, haka kuma, ya kamata a tabbatar da amfanin hanyoyin sama da na kasa wajen shiga kasashen dake bukatar taimako. Sabo da matakin rufe hanyoyin zai haifar da karin barazana, da ja da bayan ayyukan hana yaduwa da yin rigakafi kan cutar Ebola. (Maryam)