An kira wannan taro a ran 4 ga wata a birnin Geneva, wanda ya samu halartar mutane kimanin 200, ciki hadda manyan jami'an kasashen da suke fama da cutar, wakilan wadanda suka kamu da cutar da kuma masana a fannoni daban-daban da dai saruansu. Wannan ya kasance karo na biyu da WHO ta kira irin wannan taro cikin wata daya kan dabaru da allurar yaki da cutar Ebola. A cikin sanarwar da aka bayar bayan taron, an ce, dabaru da allura da aka yarda a yi amfani da su, ko da yake ba a yarda da yin amfani da su don jinyar wadanda suke kamu da cutar ba tukuna, amma an yi gwajinsu kan dabbobi tare da samun sakamako mai kyau. Shi ya sa kasashe daban daban za su gaggauta kimanta wadannan fasahohi da magunguna, ta la'akari da hali mai tsanani da ake ciki yanzu game da cutar Ebola. (Amina)