in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Saliyo ya samu koma baya sakamakon barkewar Ebola
2014-09-11 10:52:01 cri

Ministan kudi na kasar Saliyo Kelfalla Marah ya ce, barkewar cutar Ebola a kasar ta Saliyo, ya haifar da koma bayan tattalin arzikin kasar, kuma ya yi sanadiyyar gwmanatin kasar ta yi hasarar dalar Amurka miliyan 60.

A yayin da ministan yake jawabi ga manema labarai, ya bayyana cewar, wani hasashen da aka yi, ya nuna cewar, bunkasar tattalin arzikin ta Saliyo ta kai mizanin 11.3 bisa dari , to amma yanzu maganar da ake yi bunkasar tattalin arzikin kasar ta yi kasa da kashi 7 bisa dari, saboda barkewar cutar Ebola, wacce ta haddasa rurrufe wuraren gudanar da hada-hadar kasuwanci a kasar.

Ministan kudi na Saliyo ya ce, a halin da ake ciki jiragen sama sun dakatar da zirga-zirgarsu a yankin, kuma sannan ga matsalar hauhawar farashin kayayyakin masarufi, da kuma matsalar karancin kudaden shiga, kana a daidai lokaci guda ita kuma cutar ta Ebola na ci gaba da yaduwa.

To amma ministan ya ce, shugaban kasar ta Saliyo ya bayar da umurnin fitar da dalar Amurka miliyan 2.2 domin a dauki mataki kan matsalar da kasar ta shiga, da zimmar samar da mafita ta gari. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China