in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon zai kira taro domin kara karfin matakan tunkarar Ebola
2014-09-10 12:58:24 cri

Babban sakatare na MDD Ban Ki-moon ya shirya kiran wani taron shugabannin kasashe a babbar hedkwatar MDD dake New York, a karkashin wani babban taron MDD da za'a yi a wannan shekarar domin jaddada bukatar gaggawa da ake da ita ta daukar matakin da ya dace, domin tunkarar barkewar cutar Ebola a yankin Afrika ta yamma.

kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce, an yanke shawarar gudanar da taron ne bayan da babban sakataren MDD ya shaidawa shugaban kasar Amurka Barack Obama ta wayar tarho cewar, yana shirin kiran babban taron a lokacin zaman bataron MDD domin jaddada bukatun gwamnatoci da kuma matakan da ya kamata gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu, da kamfanoni wadanda ba na gwamnati ba, da hukumommin koyarwa ya cancanta su dauka, domin tunkarar cutar ta Ebola.

Za dai a fara gudanar da zaman babban taron shekara-shekara na MDD, mai mambobi 193, a ranar 24 ga watan Satumba, kuma za'a yi tsawon mako guda ana gudanar da taron.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce, idan aka kwatanta da tarihin cutar a cikin shekaru 40, a yanzu cutar Ebola ta yi tsanani, kuma kawo ya zuwa yanzu cutar mai saurin kisan bil'adama ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 2,288, daga cikin adadin mutane 4,269 da suka harbu da cutar tun bayan barkewar cutar a Guinea, Liberia, Sierra Leone da Nigeria. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China