A ranar 29 ga watan Agustar da ya shude ne dai mahukuntan kasar ta Senegal suka bayyana wannan matashi dan asalin kasar Guinea, a matsayin mutum na farko da ke dauke da cutar Ebola da aka gano a kasar, tun barkewar ta a wasu kasashen yammacin Afirka a watan Fabrairun bana.
Wannan matashi dai ya shiga kasar Senegal ne daga kasar Guinea tun kafin an rufe iyakar kasashen biyu, kuma kafin hakan an ce ya yi cudanya da wadanda suka kamu da cutar Ebola a Guinea.
Bayan da hukumar kiwon lafiyar kasar Senegal ta gano hakan ne aka fara yi masa magani, a wani wuri da aka kebe domin hana yaduwar cutar, aka kuma killace wadanda suka yi cudanya da shi bayan shigar sa kasar su 67. (Maryam)