in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Guinea na fatan sanya kafofin watsa labarai cikin shirin yaki da Ebola
2014-09-10 11:02:54 cri

Shugaban kasar Guinea, Alpha Conde ya gayyaci a ranar Talata kafofin watsa labarun kasarsa da su kara dukufa sosai wajen yaki da annobar cutar Ebola da ke shafar kasar Guinea tun yau fiye da watanni bakwai.

A yayin ganawarsa tare da 'yan jaridan kasar Guinea da na kasashen waje, shugabannin kafofin watsa labarai da kuma mambobin kungiyoyin 'yan jarida, shugaba Conde ya jaddada cewa, yaki da cutar Ebola wani muhimmin yaki ne da ke bukatar taimakon dukkan 'yan kasa baki daya, har da 'yan jarida.

A kasar Kenya kuma, shugaban kasar Uhuru Kenyatta ya bayyana a ranar Talata cewa, gwamnatinsa za ta kebe dalar Amurka miliyan daya domin taimaka wajen yaki da cutar Ebola a cikin wasu kasashen yammacin Afrika.

Mista Kenyatta ya nuna a cikin wata sanarwa cewa, annobar Ebola, babban bala'i ne kuma mai cike da sarkakiya, kuma cutar ta janyo mugun tasiri ga tsarin kiwon lafiya na kasar Kenya.

A wani labari na daban, ministocin kiwon lafiya na kungiyar SADC sun dauki niyyar kaddamar da wasu muhimman ayyuka cikin hadin gwiwa, har da matakin kebance masu bulaguron da suka fito daga kasashen yammacin Afrika da cutar ta fi kamari. Ministocin kiwon lafiya na kungiyar SADC sun shirya wani taron gaggawa a kasar Zimbabwe domin tattauna kan hanyoyin da za'a dauka na ganin an ci nasara kan annobar cutar Ebola. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China