Ya ce dukkanin mutanen da suka mutu ko aka tabbatar sun kamu da cutar suna zaune ne a yankin Gera dake jihar Equateur ta kasar.
Tun dai ranar 2 ga watan nan na Satumba ne hukumar kiwon lafiya ta duniya, ta bayar da wata sanarwa dake tabbatar da bullar cutar Ebola a kasar ta Congo Kinshasa, ko da yake an ce hakan ba shi da nasaba da yaduwa cutar, a wasu kasashen dake yammacin Afirka a halin yanzu. (Zainab)