in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da EU za su taimakawa Saliyo wajen yaki da cutar Ebola
2014-09-09 10:31:34 cri

Babban darakta a cibiyar yaki da cututtuka da ba da kariya ta kasar Sin Dr. Wang Yu, ya ce, kasarsa na shirin kafa wani dakin gwajin cutar Ebola a kasar Saliyo, domin taimakawa kasar a yakin da take yi da yaduwar cutar ta Ebola.

Dr. Wang ya kara da cewa, za a kafa dakin gwajin da wata cibiyar bincike ta musamman ne a asibitin sada zumuntar kasashen biyu dake wajen birnin Freetown, fadar gwamnatin kasar. Baya ga wata cibiyar ta gwaji ta musamman da a nan gaba, Sin za ta kafa da hadin gwiwar kasashen yammacin Afirka.

Tuni dai kwararrun da Wang ya jagoranta zuwa kasar ta Saliyo suka zanta da shugaba Ernest Bai Koroma, da kuma sabon ministan lafiyar kasar Abu Bakarr Fofanah.

Yayin ganawar, shugaba Koroma ya godewa kasar Sin bisa tallafin da take baiwa kasarsa, musamman ma a wannan mawuyacin lokaci.

A wani ci gaban kuma, hukumar gudanarwar tarayyar Turai ta EU ta alkawarta samar da kudi sama da dalar Amurka miliyan 6 ga kungiyar AU, domin ci gaba da yaki da cutar Ebola a yammacin Afirka.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce, za a yi amfani da kudaden ne wajen tallafawa sabon shirin da za a kaddamar na yaki da cutar, shirin da aka yiwa lakabi da ASEOWA.

Shirin wanda za a kafa helkwatarsa a kasar Liberiya, wanda kuma za a shafe watanni 6 ana aiwatar da shi dai zai kasance kari, kan sauran shirye-shiryen da ake aiwatarwa game da dakile yaduwar cutar ta Ebola. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China