in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi kira da a dage haramcin tafiye-tafiye bisa dalilin Ebola
2014-09-09 10:36:22 cri

Kwamitin zartaswa na kungiyar tarayyar Afrika AU, bayan wani taronsa a ranar Litinin a birnin Addis Abeba na kasar Habasha ya mai da hankali sosai kan annobar cutar Ebola, kuma ya yi kira da a dage haramcin tafiye tafiye, amma tare da jaddada mihimmancin yin amfani da matakan da suka dace domin dakatar da yaduwar cutar. Wannan zaman taron gaggawa, da ya gudana a hedkwatar kungiyar AU, na da ma'anar karfafa kokarin da ake cikin hadin gwiwa wajen yaki da cutar Ebola, dake afkwa wasu kasashen yammacin Afrika.

A cikin wata sanarwar da aka fitar kafin taron, AU ta bayyana cewa, kwamitin zartaswarta ya tabo batutuwan dake da nasaba da matakan da suka shafi hana jiragen sama zuwa kasashen da cutar ta fi kamari, rufe kan iyakokin ruwa da na kasa, da kuma nuna kyama ga kasashen da cutar ta fi shafa da al'ummominsu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China