in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata tawagar likitocin Cuba za ta taimaka wajen yaki da cutar Ebola a yammacin Afrika
2014-09-13 16:16:34 cri
Kasar Cuba ta sanya hannu kan kokarin kasa da kasa dake manufar yaki da yaduwar cutar Ebola a yammacin Afrika. Ministan kiwon lafiya na kasar Cuba, Roberto Morales ya yi wannan sanarwa a birnin Geneva na kasar Suisse, a yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da darektar kungiyar kiwon lafiya ta duniya (OMS), Margaret Chan. Kasar Cuba, da ita shahara kan kwarewarta a fannin kiwon laiya, za ta tura wata tawagar ma'aikatan lafiya dake kunshe da mambobi 165, wadanda suka hada da dokta 62 da malaman kiwon lafiya 103, dake kwarewa ta kusan shekaru 15 a wannan fanni a cikin kasashen yammacin Afrika dake fama da Ebola, in ji mista Morales.

Dukkan mambobin tawagar sun taba aiki a kasashen waje, inda suka fuskanci bala'u daga indallahi da na cututtuka, in ji ministan tare da bayyana cewa wannan tawaga za ta kwashe watanni shida a shiyyar yammacin Afrika tun daga farkon makon watan Oktoba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China