in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bude taron gaggawa kan cutar Ebola a babban birnin Habasha
2014-09-09 11:03:55 cri

Kungiyar tarayyar Afrika AU ta bude wani taro na gaggawa na majalisarta, a birnin Addis Ababa, fadar gwamnatin kasar Habasha, domin samar da dunkulallar manufa ta bai daya, wace za ta samar da takamaiman matakan da za su taimakawa Afrika dakile annobar Ebola.

A yayin taron, kungiyar ta yi amana a bisa cewar, mambobin kungiyar za su yi aiki tare domin tallafawa kasashen da cutar ta Ebola ta fi kamari.

Taron dai an shirya shi ne domin bukatar dake akwai na kowa ya fahimci, shin mene ne cutar Ebola, da kuma sanin matsayin matakan da aka rigaya aka dauka domin tunkarar cutar ta Ebola, mai tsananin hadari ga rayuwar bil'adama.

Ana sa rai taron zai samar da matakai na nahiyar Afrika, wadanda ake sa ran za su yi tasiri wajen takawa cutar Ebola birki. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China